Amnesty ta samar da manhajar Detekt

Image caption Akwai manyan manhajojin leken asiri da satar hotuna

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta samar da wata manhajar kwamfuta da zata iya gano manhajojin da gwamnatoci ke amfani da su wajen leken asirin ayyukan masu fafutuka da kuma abokan adawa na siyasa.

Kungiyar ta ce ana bukatar manhajar mai suna Detekt, saboda a wasu lokuta, manhajojin da suke bai wa kwamfutoci kariya daga hadura basa iya hana manhajojin leken asiri.

Kungiyar ta ce gwamnatoci da yawa suna amfani da manyan manhajojin leken asiri da suke iya satar hotuna daga na'urar daukar hoto dake jijin kwamfutoci, ko kuma nadar bayanan sauti daga makirfo.

Amnesty International ta na so a kara daukan mataki na lura da aiki da manhajojin leken asiri da gwamnatoci ke amfani da su.

Wata jami'ar kungiyar ta Amnesty, Tanya O'Carroll ta ce masu kera manhajojin leken asiri suna daukar lokaci suna gwaji don tabbatar da manhajojin kare kwamfutoci daga hadura basa iya ganin manhajojin leken asirin a cikin kwamfutocin.

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Akwai manhajojin leken asiri da ke nadar bayanan sauti ta makirfon kwamfuta

Kimanin shekaru biyu kenan da kirkirar manhajar Detekt, kuma an yi zubin farko na manhajar ne ya yi aiki a kwamfutoci masu amfani da manhajar Windows, saboda a kasarin mutane da a ka fi yi musu leken asiri, suna amfani da manhajar Windows ne.

Gwamnatoci masu kama karya da yawa sun dade su na amfani da manhajojin leken asirin, kuma yan zu abin yana kara yawa a wajen gwamnatocin demukradiyya suma.

An gano ire-iren manhajojin leken asiri a kwamfutocin masu fafutuka a Bahrain, da Syria, da Ethiopia, da Vietnam, da Jamus, da Tibet da Koriya ta Arewa da sauran Kasashe masu yawa.

Sai dai Farfesa Alan Woodward na jami'ar Surrey, wanda kuma yake bai wa gwamnatoci shawarori a kan al'amuran tsaro, ya na mamakin yadda kungiyar Amnesty da wadanda take aiki tare da su za su iya tafiyar da manhajar Detekt.