Majalisar Wakilai ta yi watsi da dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal

Majalisar wakilan Nigeria, ta yi watsi da bukatar shugaba Jonathan na tsawaita dokar ta-baci a wasu jihohin arewa maso gabashin kasar.

Majalisar ta ce dokar ta-bacin da aka kafa a jihohin Yobe da Borno da kuma Adamawa ba ta yi tasiri ba a cikin watanni 18 da aka kafa a don haka babu bukatar a kara tsawaita dokar.

Mai magana da yawun majalisar wakilai, Zakari Mohammed wanda ya shaida wa manema labarai matsayin da majalisar ta cimma, ya bukaci Mr Jonathan ya yi amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi ya tura karin jami'an tsaro a wuraren da ake rikici a kasar.

Sashe na takwas na kundin tsarin mulkin Nigeria ya bai wa shugaban kasa damar aika dakarun tsaro a duk inda ake fama da rikici.

Matakin majalisar wakilan ya biyo bayan yinkurin wasu 'yan sanda na hana kakakin majalisar, Aminu Tambuwal da wasu 'yan majalisar shiga zauren majalisar.

Daga bisani, Tambuwal da sauran 'yan majalisar sun kutsa cikin zauren majalisar da karfin tuwo duk da barkonon tsohuwa da 'yan sanda suka harba.