An rufe babban masallacin Mombasa a Kenya

Hakkin mallakar hoto afp getty
Image caption 'Yan sanda sunata kai samame a masallatai a Mombasa

Hukumomi a kasar Kenya sun rufe babban masallacin birnin Mombasa sannan suka umarci musulmin da suka je yin sallah a masallacin da su tafi wani masallacin.

An kashe akalla mutum guda a taho-mu-gamar da aka yi ranar Alhamis, bayan jami'an tsaro suka far ma Musulmai a wannan makon.

AbdusSamad Shariff Nassir, wani musulmi ne, dan majalisar dokoki daga birnin na Mombasa, kuma ya ce tura fa ta fara kai wa bango.

Nasir ya ce "A al'adance idan ka takurawa mutane za su yi hakuri, za su saka kuka, amma idan ka matsanta musu to fa za su mayar da mummuna martani."

Masu aiko da rahotanni sun ce rufe masallacin zai kara zaman dar-dar din da ake yi a birnin na Mombasa.