Nijar: Hama Amadu ya rasa mukaminsa

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Hama Amadu ya gudu daga kasarsa ne bayan an cire mushi rigar kariya

A jamhuriyar Nijar, kotun tsarin mulkin kasar ta ce mukamin shugaban majalisar dokokin kasar ya fita daga hannun Malam Hama Amadu.

Kotun ta ce mukamin ya kubuce ma shi ne saboda gudu da ya yi, inda ya bar mukamin na sa lokaci mai tsawo ba tare da wata hujja ba.

Saboda haka kotun ta ce wajibi ne a yanzu 'yan majalisar su zabi wani sabon shugaba a cikin kwanaki 15.

Mista Hama Amadu ya gudu daga kasar ne a watan Agusta bayan an cire mushi kariyar da yake da ita, domin ya gurgana a gaban kotu bisa zarginsa da hannu a cikin badakalar sayen jarirai daga Najeriya.