'Za a iya rikici a zaben 2015 a Nigeria'

Image caption Farfesa Jega na INEC na fuskantar matsin lamba

Zabukan 2015 da ke tafe a Nigeria na kan hanya ta rashin tabbas da kuma rikici, idan har ba a dauki mataki ba, kamar yadda wata kungiyar ta yi gargadi.

Kungiyar International Crisis Group wadda ta yi wannan gargadin ta ce akwai bukatar a dauki mataki domin magance fuskantar rikici irin wanda ya auku bayan zaben da aka gudanar a shekara ta 2011.

A cewar kungiyar "Nigeria na cikin hadarin fuskantar tashin hankali" a zaben watan Fabarairu idan har ba a dauki matakan kwantar da kura ba.

Kungiyar ta ICG ta ce za a iya samun tashin hankali idan har jam'iyyar APC ta fadi zabe a wasu jihohin arewacin kasar kamar yadda za a iya fuskantar rikici a kudancin kasar idan jam'iyyar PDP ta sha kaye.

Kungiyar kuma ta shawarci 'yan siyasa su iya bakinsu a wajen kamfe su guji kalaman da za su ta da zaune tsaye.

Kungiyar ta kuma bukaci shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya dauki matakan tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin kasar sannan kuma ya tabbatar da cewar an yi zabe a daukacin jihohin kasar a 2015.