Llittafi mai magana don talakkawa a Ghana

Litattafai masu magana don talakkawan Ghana Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Litattafai masu magana don talakkawan Ghana

Gwajin wannan shiri zai kunshi litattafan masu magana 2,000, to amma za a karo wasu idan shirin ya samu nasara.

Za a bayar da Komputoci na hannu masu magana ga wasu daga cikin al'ummomin dake fama da matsanancin talauci don taimakawa wajen yada bayanai masu muhimmanci na ceton rayuka.

Litattafan masu magana za su baiwa iyalai damar kunna wasu maganganu da aka nada aka adana tare kuma da ba su damar nadar bayanai da kan su, wanda za su aika ma wasu ko kuma yin sharhi a kan wasu bayanan.

Masu wannan shiri sun yi niyyar yin amfani da wata hanya ta ilimantar da mutane game da cutar Ebola, yadda za su bullo ma wasu cututtuka na shuke-shuke da muhimmanci shayar da nonon Uwa ga jarirai da dai sauran wasu batutuwan.

Kungiyoyin Unicef da wani kamfani mai tsara manhajar Komputa ARM su ne ke bayar da mafi rinjayen kudi dola 750,000 na wannan shiri.

An yi shirin tafiyar da shirin a tsawon shekaru biyu da rabi, yayinda za a rinka sabunta bayanan dake cikin wannan shiri sau daya cikin a ko wadanne makonni biyar.

Kudin da za a bayar, za su dauki nauyin samar da litattafan dubu biyu da ma'akatan da za su koyar da su, kuma ana da burin mutane kimanin 40,000 za su yi amfani da su.

Litattafan dai ba su da allo kuma an shirya su ne ta yadda mutane wadanda ba su je makaranta ba za su ji saukin amfani da su wajen saurare da nadar magana.

Literacy Bridge - Kungiyar dake tafiyar da shirin na gwaji - ta ce litattafan na ta masu magana, an shirya su ne don amfanin mutanen da mai yiwuwa ba za su iya karatu ba.

Daraktan kungiyar ya gaya ma BBC cewar "litattafan za su yi magana da mutum ne cikin harshen sa da kuma irin karin harshen mutum kuma zai nemi mutum ya latsa wani makyalli don yin duk abinda yake so."

Karin bayani