An samu saukin yaduwar Cutar Ebola a Guinea

Hakkin mallakar hoto AFP

Babban jami'in Hukumar Lafiya ta duniya, wato WHO a kasar Guinea yace, yanzu an dan samu saukin yaduwar Cutar Ebola a fadin kasar.

Sai dai kuma jami'in, Guenayel Rodiye ya ce, duk da haka ana samun barkewar cutar Ebolan jifa-jifa a yankin kudu maso gabashin kasar ta Guinea.

Ya kuma ce, ana bukatar kwararru daga kasashe daban-daban domin hana karuwar barkewar cutar.

Wakiliyar BBC da yanzu haka take Guinea ta ruwaito cewa watanni takwas bayan barkewar cutar Ebola har yanzu wasu a kasar ta Guinea ba su ma yarda cewa, Ebolan wata cuta ce ba.