Tambuwal: Zan amsa gayyatar jami'an tsaro

Yamutsi a majalisar Wakilan Nijeriya Hakkin mallakar hoto peoples daily
Image caption Yamutsi a majalisar Wakilan Nijeriya

A Nijeriya, shugaban majalisar wakilai ta kasar, Hon. Aminu Tambuwal ya ce a shirye yake ya amsa gayyatar da hukumomin tsaro a kasar za su yi ma shi a kan kowanne irin batu da za a bukace shi ya yi bayani akai.

Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi kan sha'anin yada labarai, Imam Imam ya fitar, a game da rahotannin dake cewa Sufeta Janar na 'yan sandan kasar ya umurce shi da ya gurfana a shedkwatar 'yan sandan, in ya ki kuma, to za a kama shi.

Kakakin Majalisar a cikin sanarwar, ya kuma nuna rashin jin dadi da abinda ya kira rashin kwarewa da aiki, da 'yan sandan Najeriya suka nuna lokacin da suka hana shi shiga cikin majalisar don yin wani zama mai muhimmanci.

Ya kuma musanta hujjojin da 'yan sandan suka bayar, cewa Aminu Tambuwal din ya je majalisar ne da wasu 'yan bangar siyasa, inda yace abin takaici ne a bayyana abokan aikinsa a majalisar da suka je yin zaman na musanman a matsayin 'yan bangar siyasa.

Sai dai da BBC ta tuntubi mai magana da yawun 'yan Sandan Nigeria Emmanuel Ojukwu, ya ce 'yan sanda basu gayyaci kakakin majalisar ba.

Karin bayani