Taraba: Mataimakin Gwamna ya kori kwamishinoni

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Siyasar jahar Taraba ta kasance cikin rudani tun bayan hatsarin Gwamna Danbaba Suntai

Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya na cewa mataimakin gwamnan jihar da kotu ta mayar kan mukaminsa ya soma aiki.

Ya kuma fara ne da korar dukkan masu rike da mukamai da aka nada tun bayan hadarin jirgin sama da gwamnan jihar Danbaba Suntai ya yi.

Alhaji Sani Abubakar Danladi ya kuma nada sabon sakataren gwamnati da kuma babban jami'in ma'aikata a ofishin gwamnan jihar.

To sai dai ya kama aiki ne a matsayin mataimakin gwamna, amma ba mukaddashin gwamna ba.