Babu wadatattun likitocin yara a Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Likita daya ya na duba yara kimanin 50 a Afrika

Likitocin yara kanana na wasu kasashen Afrika sun kammala wani taro a Yaounde, na kasar Kamaru domin shawo kan matsalar tamowa dake addabar kananan yara.

Alkalumman hukumar kiwon lafiya ta duniya sun nuna cewa yaro guda a cikin ukku 'yan kasa da shekaru biyar na fama da rashin mikewar gabobi a kasashe masu tasowa sanadiyar tamowa.

Akan haka ne aka cimma matsayar maida hankali da ciyar da yara abinci mai gina jiki.

Mahalarta taron sun koka da karancin likitocin yara a Nahiyar Afrika, inda suka ce likita daya yana duba lafiyar kimanin yara 50.