Iran: Ana tababa a kan cimma yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Iran ta ce shirin ta na sarrafa nukiliya bana kera makamai bane

Akwai tababa a game da kokarin cimma wa'adin da aka gindaya na ranar litinin na kulla yarjejeniya da Iran kan shirin ta na nukiliya.

A wajen tattaunawar a Vienna, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce har yanzu a kwai wagegen gibi da yakamata a cike kafin a cimma wata yarjejeniya akan butun sarrafa nukiliyar a kasar Iran.

Ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier ya ce akwai yiwuwar samun nasara, amma idan kasar Iran ta so haka.

Babbar takaddamar dai yanzu, ita ce girman aikin sarrafa sinadarin nukiliya a kasar Iran anan gaba, da kuma lokacin da kasar zata samu saukin takunkumin da aka sanya mata.