Faransa za ta kara sansanin soji a Nijer

Hakkin mallakar hoto

Faransa ta ce za ta bude wani sabon sansani soji a Jamhuriyar Nijer, domin ci gaba da tunkarar matsalar tsaro a Nijer da sauran kasashen yankin Sahel.

Fira-ministan Faransan ne, Manuel Valls, ya fadi hakan a Yamai a ziyarar aikin da ya kai ma Nijer.

Mista Valls ya tattauna da Shugaba Mouhammadou Issoufou na Nijer game da sha'anin tsaron, musamman rawar da rundunar tsaro ta Barkhane ke takawa wajen yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Ya ce kasar Nijer kadai ba za ta iya magance matsalar ta'addanci da ke addabar yankin ba, saboda haka ne Faransan za ta kara sansanin soji a kasar.

A nasa bangaren shugaban Nijer ya ce kasashen biyu za su yi aiki tare domin yaki da 'yan ta'adda.

Fira-ministan ya isa Nijar din ne bayan ya ziyarci kasar Chadi, duk dai akan maganar tsaron.

Karin bayani