An cafke masu satar shafukan Komputa

Yan Sandan Brittaniya Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Yan Sandan Brittaniya

A wani samame da aka kai Brittaniya da wasu kasashen Turai, an cafke masu satar shafukkan Komputa na mutane a lokacinda suke aiki da Komputar.

Jami'ai ne daga hukumar yaki da miyagun laifukka ta kasa ta kai wannan samame na cafke miyagun mutanen nan dake kwace ma mutane shafin su na Komputa a lokacinda suke aiki da ita.

Mutane goma sha-biyar ne aka cafke wadanda suka hada da wasu mutanen hudu a Brittaniya masu alaka da mugun laifin nan.

'Yan sanda sun ce mutanen suna amfani da wata manhaja ne mai sarrafa kan ta - wadda take ba su damar satar bayanan jama'a.

Sauran samamen na kame irin wadannan mutane an kai shi ne a kasashen Estonia da Romania da Latvia da Italy da kuma Norway.

Wannan sata ta shafukkan Komputa wadda a wasu lokutta ta kan bayar da damar kutsawa kamerar Komputa ta mutane ana kuma kiran ta " hanyar satar bayanai", ko kuma "ratting".

Wannan hanya dai ta samo suna ne daga tsutsar nan ta Komputa da a kan yi amfani da ita wajen yin kuutse a Komputar mutane.

Amfani da wannan tsutsar don leken abinda wasu ke yi a Komputar su ta hanyar Kamera ta Komputar ba tare da sanin su ba, yana kara zama ruwan dare, a cewar wani shafin Internet da gwamnatin Brittaniya ke daukar nauyin tafiyar da shi wanda ake kira "ka saki jikinta a Internet babu wanda yake yi ma kuutse."

Hukumar yaki da miyagun laifukkan ta kasa ta ce ta damke wani mutum dan shekara 33 da haihuwa da kuma wata Matar 'yar shekaru 30 da haihuwa a garin Leeds.

A wata sanarwa da ta bayar, hukumara dake yaki da miyagun laifukka ta ce, ana samun damar yin kutse ne a Komputar mutane a lokacinda aka zalzale su cewar su latsa wata mahada wadda ake nuna hoto ne ko video ko kuma a fake da cewar wani file ne, to amma a rashin sani, hanya ce ta jefa ma mutum wannan tsutsa ta Komputa.

Alokutta da dama, wadanda ba su sani ba suka latsa wani wuri suka jefa wannan tsutsa ta Komputa, ba za su ga wata alama ba da za ta nuna cewar, wata tsutsa ta shiga cikin Komputar su.

Karin bayani