Ana zaben Shugaban Kasa a Tunisia

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan Tunisiya na kada kuri'unsu a zaben shugaban Kasar na farko tun daga juyin juyin halin shekarar 2011 wacce ta harzuka bore a daukacin yankin kassahen larabawa

'Yan takara fiye da 25 ne zasu fafata amma shugaban kasar mai ci Moncif Marzouki da kuma Beji Essebsi shugaban masu adawa da masu kishin addinin Islama sune akan gaba

A watan oktoba akai zaben 'yan majalisun dokoki

Idan ba a sami dan takarar da ya lashe fiye da kashi hamsin cikin dari na kuri'un da aka kada ba. za a tafi zagaye na biyu a ranar 31 ga watan Disamba