APC na son a yi bincike kan kutse a ofishinta

Image caption APC ta ce farmakin ba zai hana ta yunkurin kawar da PDP daga mulkin Nigeria ba

A Nigeria, jam'iyyar adawa ta APC ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa don tantance dalilan da suka haddasa farmakin da wasu jami'an tsaron farin kaya da sojoji suka kai a ofishinta da ke a Lagos a ranar Asabar.

Jam'iyyar ta APC, wadda ta ce ba ta yi mamakin farmakin ba, ta bayyana lamarin a matsayin wani kokari na jefa Nigeria a rudani.

Ta kara da cewa duk wani matsayi da jami'an tsaro za su dauka a kanta ba za ta yi mamaki ba saboba a cewarta, suna yi wa gwamnatin PDP mai mulkin kasar ne.

Kazalika, jam'iyyar ta APC ta ce wannan farmaki ba zai sa ta kauce daga alkiblar da ta sa a gaba ba ta ganin ta kwace mulki a hannun jam'iyyar PDP.

Wasu jami'ai da ake zargi na hukumar tsaro ne ta masu farin kaya ne, wato SSS suka kai samame a daya daga cikin ofishin jam'iyyar a Lagos inda ake zargin sun lalata na'urori da sauran kayayyaki, tare da yin awon-gaba da wasu ma'aikata da ke aiki a ofishin jam'iyyar.

Karin bayani