'Yan Boko Haram sun kai hari a Damasak

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Shekau ya ce babu sulhu da gwamnatin Nigeria

Rahotanni daga garin Damasak a jihar Bornon Nigeria na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin da safiyar ranar Litinin.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa marahan sun shiga garin a motoci kirar Hilux da babura, haka kuma wasu a cikinsu na sanye da kakin soji wasu kuma sanye da kayan gida.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin, Sanata Maina Ma'aji Lawan ya tabbatar wa da BBC batun kai harin amma babu cikakkun bayanai game da lamarin.

Sanata Lawan ya kara da cewa wasu iyalai tuni suka fara tsallaka kogi domin neman mafaka a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da su.

Wannan harin na zuwa ne bayan da a cikin makon da ya wuce 'yan Boko Haram suka hallaka mutane kusan 100.