Za a kara wa'adin yarjejeniya da Iran

Taron shawara game da nukiliya na Iran Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Taron shawara game da nukiliya na Iran

Amurka ta gaya ma Iran cewar lokaci ya yi da za a kara tsawaita wa'adin cimma yarjejeniya a kan Shirin ta na Nukiliya.

Jami'ai sun ce Sakataren harkokin wajen Amurkar John Kerry ne ya ba da shawarar haka ga Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Zarif lokacin shawarwarin a Vienna.

Amurkar dai ta musanta wasu bayanai da aka ce Iran din ta bayar na cewa an sasanta kan wasu batutuwa na siyasa. Amurkar da Brittaniya da Faransa suna fatar takaita ayyukan nukiliyar ne na Iran don a janye takunkumin da aka garkama ma ta.

Wasu 'yan kasar ta Iran dake bayyana ra'ayinsu a kan batun, sun ce tunda aka dauki tsawon lokaci haka akwai alamun za a cimma yarjejeniya.

Karin bayani