Wa'adin yajejeniya kan Nukiliyar Iran ya kare

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kasar Iran ta ce shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne

Jami'an diplomasiyya daga manyan kasashen duniya shida da kuma kasar Iran suna kokarin ganin an cimma yarjejeniya kan shirin Nukiliyar Iran.

Jami'an sun bayyana cewa har yanzu manyan sabanin da aka samu tun da fari ba a warware su ba, abin da ya sa suka ba da shawarar a kara lokaci.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, Philip Hammond, ya ce yana so a cimma karin wa'adin a tattaunawar ta Vienna, sai dai baya so ya sa wa mutane rai kan abin da ba lallai ya tabbata ba.

Kasashen Amurka da Burtaniya da China da Rasha da Faransa da kuma Jamus na son Iran ta dakatar da shirinta na Nukiliya, idan tana so a janye takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata.