Mutane 78 ne suka mutu a kasuwar Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bam din ya tashi ne kasuwar Monday

Ma'aikatan asibiti a Maiduguri sun ce mutane 78 ne suka mutu bayan wasu hare haren kunar bakin wake biyu da aka kai wata kasuwa mai cike da hada- hada.

Ganau sun ce fashewar farko ta faru ne a lokacin da maharan suka daurawa wata mace mai tabin hankali abubuwan fashewar a jikinta.

A lokacin da mutane suka zo taimaka mata, sai wata 'yar kunar bakin waken ta tayarda bam din dake jikinta.

Ana zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai hare haren

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da rahotanni suka ce 'yan Boko Haram sun kwace garin Damasak da ke karamar hukumar Mobbar a jihar ta Borno.