Ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 25 ga watan Nuwamban kowace shekara domin tunawa da matsalar cin zarafin mata a kasashen duniya.

A cewar Majalisar matsalar babban ce a tsakanin al'umomi daban-daban na duniya, da ke tauye 'yancin mata ta fuskar ilimi da kiwon lafiya da tattalin arziki da kuma zamantakewa.

A Najeria masu fafutukar kare hakkin bil'adama da hana cin zarafin mata sun nuna damuwa game da yadda matsalar fyade take karuwa a kasar.

Kuma sun bayyana damuwa game da matsalar fyade da kuma yadda ake sace mata da kuma 'yan mata musamman a yankin arewa-maso-gabashin kasar.