Majalisar Niger za ta zabi sabon Kakaki

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Hamma na samun mafakar siyasa a kasar Belgium

'Yan majalisar dokoki a jamhuriyar Nijar za su ka da kuri'a domin zaben sabon shugaba wanda zai maye gurbin Hamma Amadu a ranar Litinin.

Hakan ya biyo bayan umurnin da kotun tsarin mulki kasar ta bayar a makon jiya, inda ta ce bai cancanta Hamma ya ci gaba da rike mukamin kakakin ba saboda kwashe tsawon lokaci ba ya kan kujerarsa.

Fiye da watanni biyu kenan da Hamma ya tsere daga Nijar bayan an tube masa rigar kariya, biyo bayan zarginsa da hannu a safarar jarirai daga Najeriya.

Sai dai Hamma ya yi ikirarin cewa ana barazana ga rayuwarsa.