An nada sabon kakakin Majalisa a Nijar

Amadou Salifou, Kakakin Majalisar Dokokin Nijar
Image caption Amadou Salifou, Kakakin Majalisar Dokokin Nijar

A jamhuriyar Nijar majalisar dokokin kasar ta zabi Alhaji Amadou Salifou a matsayin sabon kakakin majalisar inda ya samu kuri'u 71 daga cikin 76 da aka kada.

Sai dai 'yan adawa ba su kada kuri'ar zaben nasa ba, suna masu cewa ba a bi ka'ida ba.

Har ma sun shigar da bukatar yanke wa gwamnati kauna, kuma a ranar Laraba ne majalisar za ta kada kuria a kan wannan bukata.

Amadu Salifou, mamban kawancen ARN ne mai adawa, amma ya bijire domin mara wa shugaban kasa baya, tare da wasu jigogin jam'iyar MNSD Nasara irin su Albade Abouba da suka karbi mukamai a cikin gwamnati a watan Agustan bara.

Zaben sabon kakakin dai ya biyo bayan hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke ne a makon jiya, inda ta ce bai dace Malam Hama Amadou ya ci gaba da kasancewa shugaban majalisar dokokin ba, ganin cewa ya bar kujerarsa ba tare da wata hujja ba.

A karshen watan Agustan da ya gabata ne dai, Hama Amadou ya fice daga Nijar zuwa Faransa inda yake gudun hijira, sakamakon zargin da ake ma shi na hannu a wani abun kunya na sayo jarirai daga Najeriya.

Karin bayani