An yi watsi da Bama - 'Yan gudun hijra

Harin 'yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harin 'yan Boko Haram

A Najeriya 'yan gudun hijira na garin Bama dake cikin jahar Borno daya daga cikin jahohin arewacin kasar masu fama da tashin hankali na 'ya kungiyar Boko Haram, sun nuna rashin jin dadin su da kasancewar garin hanun 'yan kungiyar Boko Haram sama da watanni ukku kenan ba tare da gwamantin tarraya ta yi wani abun a zo a gani ba wajen kwato gari ba.

A tattaunawar su ta wayar tarho da Abduo Halilou, daya daga cikin shugabannin kungiyar ci gaban yankin, da ba ya so a ambaci sunansa saboda dalilan tsaro, ya yi kira ga gwamnatin tarraya da ta taimaka ta kwato wannan gari don fitar da jama'a daga cikin mauyacin halin da suke ciki.

Dan gudun hijirar yace, Bama babban gari ne da ya kunshi barikin Soji da manyan ofishin shiyya biyu na 'yan sanda.

Yace, a yanzu kusan Mata ne da Yara suka rage a garin 'yan Boko Haram din suna juyyuya su yadda suka so tun kwana casa'in da suka gabata, amma har yanzu gwamnati ba ta yi wani abu ba na kwato shi.

Karin bayani