Majalisa ta gayyaci sufetan 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana zargin 'Yan sandan Nigeria da take hakkin 'yan kasa

A ranar Talata ne ake sa ran Sufetan 'yan sandan Nigeria, Suleiman Abba zai bayyana a gaban majalisar dattawan kasar bisa harba barkonon tsohuwa ga kakakin majalisar wakilai Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye kan Hon. Tambuwal da wasu 'yan majalisa lamarin da ya janyo cece-ku ce a kasar.

Shugaban 'yan sandan Nigeriar dai bai bayyana a gaban majalisar wakilan ba, a lokacin da ta gayyace shi a ranar Juma'a.

Sai dai mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Namadi Sambo ya gana da shi bayan aukuwar al'amarin na ranar Alhamis.

'Yan sandan Nigeria dai na shan suka daga bangarori da dama tun bayan aukuwar al'amarin na ranar Alhamis