An zabi sabon kakakin majalisar Taraba

Image caption Jihar Taraba dai ta fada cikin rikicin siyasa ne tun lokacin da Gwamna Suntai ya kwanta rashin lafiya sakamakon hatsarin jirgin da ya yi.

Rahotanni daga jihar Taraba da ke Nigeria na cewa majalisar dokokin jihar ta zabi sabon kakaki domin maya gurbin kakakin majalisar da ya yi murabus.

Wanda aka zaba a matsayin sabon kakakin shi ne Dr Mark Useni domin maye gurbin Jossiah Sabo Kente.

Kazalika, majalisar dokokin ta amince mataimakin gwamnan jihar da kotu ta mayar kan mukaminsa, Alhaji Sani Abubakar Danladi, ya yi aiki a matsayin mukaddashin gwamnan jihar har zuwa lokacin da gwamnan jihar Danbaba Sunati zai samu sauki.

Jihar Taraba dai ta fada cikin rikicin siyasa ne tun lokacin da Gwamna Suntai ya kwanta rashin lafiya sakamakon hatsarin jirgin da ya yi.

Karin bayani