Kakakin majalisar Taraba ya yi murabus

Image caption Jihar Taraba dai ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da gwamna Danbaba Suntai ya kwanta rashin lafiya bayan ya yi hatsarin jirgin sama.

A Nigeria, kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Josiah Sabo Kente, ya yi murabus saboda zargin da ya yi cewa ana shirin tsige shi.

Mista Kente ya shaidawa BBC cewa ya ajiye aikinsa ne saboda a zauna lafiya a jihar.

Ya kara da cewa tun ranar da sabon mataimakin gwamnan jihar Danladi Abubakar ya hau kan kujerar mulki ya samu labarin cewa ana shirin tsige shi.

Mista Josiah Sabo Kente yana da alaka ta kurkusa da tsohon mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Garba Umar, wanda Kotun Kolin kasar ta cire a makon jiya, sannan ta ba da umarnin nada Alhaji Danladi a matsayinsa.

Jihar Taraba dai ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da gwamna Danbaba Suntai ya kwanta rashin lafiya bayan ya yi hatsarin jirgin sama.

Karin bayani