Ana cacar- baka tsakanin PDP da APC

Image caption Ba tun yanzu bane bangarorin biu ke caccakar juna

A Nigeria, babbar Jam'iyyar adawa ta APC ta maida martani dangane da sanarwar da jam'iyyar PDP mai mulki kasar ta fitar inda ta zargi 'yan adawa da yunkurin bata suna tare da cin mutuncin ofishin shugaban kasar.

A wata sanarwa da kakakin Jam'iyyar PDP Olisa Metuh ya aikewa da BBC ya ce irin yadda wasu shugabannin adawa ke sukar shugaban kasar, wata manuniya ce ga irin rashin alkibla daga bangaren 'yan adawar.

Jam'iyyar ta PDPn ta kuma zargi APC da zama babbar barazana ga tsarin mulki demukradiyya, a don haka jam'iyyar ta ce ba za ta sake zura ido ba tana kallon wasu na sukar shugaban kasar da tsarin mulki babu gaira babu dalili.

Sai dai a tattaunawar sa da BBC, Hon Faruk Adamu Aliyu wani jigo a Jam'iyyar APC ya bayyana kalaman da PDPn ta yi a matsayin soki buruzu.