An tsare tsohon Firai ministan Portugal

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mr Socrates zai ci gaba da zama a gidan yari, in ji alkali

Wani alkali a kasar Portugal ya ce a ci gaba da tsare tsohon firaministan kasar Jose Socrates yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken cin hanci da rashawa a kansa.

A ranar Juma'ar da ta gabata aka kama Mr Socrates bayan da wani biciken farko ya samu hanunsa dumu-dumu a cikin badakalar ajiye kudade ba bisa ka'ida ba da kuma bayar da cin hanci.

Bayanai daga kasar ta Portugal na cewa, tsohon Firaministan ba zai fuskanci tuhuma ba har sai an kammala binciken, abin da da ake ganin zai kai watanni takwas kafin a kammala.

Wannan lamari a cewar wakilin BBC dake Lisbon, ya girgiza fagen siyasar kasar ganin yadda za a tsare tsohon firaiministan har na wannan tsawon wannan lokaci.

Karin bayani