An yi satar fasahar wani fim a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan sandan dake yaki da satar fasaha sun tsare wasu mutane biyu bisa zargin fitar da wani fim mai suna The Expendables 3 kafin ranar da ya kamata ace an fitar da shi

Kwafi kwafin fim din ya soma yawo ne a shafin Internet daga ranar 25 ga watan Yuli

Amma a hukumance kamata ya yi ace an saki fim din ranar 15 ga watan Agusta

Jama'a kuma sun kakkalli Kwafin fim din da aka yi satar fasahar sa.

An dai tsare mutanen dan shekaru 36 da kuma dan shekaru 33 a gidajensu, sannan aka garzaya da su wasu ofisoshin 'yan sanda

Ana zargin mutanen mutanen biyu da satar fim din kafin daga bisani su sanya shi cikin internet