CAR: An nemi a sanya wa Djotodia takunkumi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Afrika ta Tsakiya ya raba dubban mutane da mulallansu

Wani kwamiti na kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a sanya wa tsohon shugaban jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, Michel Djotodia takunkumi.

Kwamitin ya nemi a yi hakan ne saboda karan tsayen da Djotodia ke yi ga yunkurin samar da zaman lafiya a kasar.

Mr. Djotodia ya karbi mulki ne bayan kungiyar 'yan tawaye ta Seleka ta hambarar da gwamnatin Francois Bozize, lamarin da ya jefa kasar cikin tashin hankali tsakanin Musulmi da Kirista.

A halin yanzu dai Mr. Djotodia na zaman gudun hijira a Benin, kuma zai iya fuskantar haramcin tafiye-tafiye da hana shi taba kudadensa da kadarorinsa.

Kwamitin sanya takunkumi zai kuma duba jerin sunayen wasu manyan mutane a kasar, ciki har da manyan jami'an soji kafin gabatar da shawarawarinsa ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.