Wani mutum ya kai jami'ar mata kara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahukuntan jami'ar dai ba su ce komai kan batun ba, sai dai sun ce za su san yadda za su bullowa lamarin cikin ruwan sanyi.

Wani mutum dan kasar Japan ya kai jami'ar mata-zalla kara saboda an ki ba shi gurbin yin karatu a cikinta.

Mutumin wanda ba a fadi sunasa ba, ya ce hana shi gurbin yin karatun da jami'ar Fukuoka Women ta yi ya sabawa 'yancin da ya bai wa kowanne dan kasar dama ya yi karatu ba tare da nuna bambanci ba.

Mutumin yana so ya karanci fannin samar da abinci.

Ya roki kotu ta bukaci jam'aiar ta biya shi fiye da dala dubu uku saboda wannan batu.

Mahukuntan jami'ar dai ba su ce komai kan batun ba, sai dai sun ce za su san yadda za su bullowa lamarin cikin ruwan sanyi.

Karin bayani