Rikicin Missouri ya bazu a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga na ganin cewar ba a yi adalci ba kan sharia'ar

Zanga-zanga kan wanke dan sanda farar fata da ake yi a Missouri ya bazu zuwa biranen Oakland da Califonia.

Sai dai zanga-zangar luman ak yi a biranen New York da Seattle kan wanke dan sanda farar fata bisa zargin kisan matashi bakar fata, Micheal Brown.

An dai baza jam'ian tsaro a Ferguson da ke jihar Missouri inda zanga zangar ta faro kwana guda bayan yanke hukuncin a ranar Litinin da daddare.

Gwamna Jihar Missouri, Jay Nixon ya ce akalla jami'an tsaro 2,200 aka tura yankin, yayin da magajin Garin na Ferguson James Knowles, ya soki jinkirin da ake samu wajen aike wa da jam'ian tsaron.