An tura karin dakaru zuwa Missouri

Ana ci gaba da baza daruruwan jam'ian tsaro a Ferguson dake jihar Missouri a kasar Amurka, kwana guda bayan da zanga zanga ta barke.

Zanga zangar ta biyo bayan matsayar da masu yanke hukunci sukadauka ne, bisa zargin habe wani matashi bakar fata da wani dan sanda farar fata ya yi.

Gwamna Jihar Missouri, Jay Nixon, ya ce akalla jami'an tsaro 2,200 aka tura yankin, yayin da Magajin Garin na Ferguson James Knowles ya soki irin jinkirin da ake samu wajen aikewa da jam'ian tsaron.

A ci gaba da zanga zangar, masu boren sun datse wata babbar hanya na dan wani lokaci a tsakiyar St. Louis, yayin da rahotanni ke cewa masu zanga zangar sun yi wata arangama da jami'an tsaro.