An harbe ma'aikatan polio hudu a Pakistan

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ma'aikatan polio da 'yan sanda fiye da 60 aka kashe a cikin shekaru biyu a Pakistan

An harbe wasu ma'aikatan Polio a kasar Pakistan, yayin da wasu uku kuma suka jikkata, a cewar Jami'ai.

Wasu da ba a san ko su wanene ba a kan babura ne suka harbe ma'aikatan mata uku da kuma direbansu namiji.

A farkon wannan watan ne aka kaddamar da shirin yaki da cutar polio a Birnin Quetta, yankin da ke fama da rikici a kasar.

An fi dora alhakin kai irin wadannan hare-hare kan masu kishin Islama da ke kallon ma'aikatan a matsayin masu leken asiri ko kuma ruwan maganin na hana haihuwa.