Tambuwal: Majalisar dattawa ta kafa kwamiti

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Ana zargin sufeto janar na 'yan sandan Nigeria da zama dan amshin shata

Majalisar Dattawan Nigeria ta kafa kwamiti mai wakilai bakwai domin ya binciki lamarin da ya kai har jami'an tsaro suka hana kakakin majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Tambuwal da sauran 'yan majalisa shiga ginin majalisar.

An bai wa kwamitin kwanaki goma domin ya mika rahotonsa ga zauren majalisar dattijai.

A makon da ya wuce ne jami'an tsaron suka harba barkono mai sa kwalla domin tarwatsa 'yan majalisar da suka yi kokarin shiga ginin majalisar da karfi.

Bayan ja-in-ja na wani lokaci, wasu daga cikin 'yan majalisar sun haura da saman kofar majalissun dokokin.

Lamarin dai ya janyo kakkausar suka kan 'yan sandan Nigeria a kan cewar suna nuna goyon baya ga bangaren shugaban kasar.