'Yan majalisa na shirin tsige Jonathan'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Nigeria na fuskantar suka daga wasu 'yan majalisa

Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya sun bi sahun takwarorinsu na majalisar wakilai wajen fara yunkurin tsige shugaba Goodluck Jonathan daga kan mukaminsa.

A wata hira da manema labarai, Sanata Abdulkadir Alkali Jajere ya ce kawo yanzu 'yan majalisar dattawa kusan 36 sun saka hannu kan takardar nuna amincewa da matakin; ciki kuwa har da 'yan jam'iyyar PDPn ta shugaban kasar.

Masu wannan yunkuri dai sun zargi Shugaba Goodluck Jonathan da keta tsarin mulki, abinda ya sa suka ce zasu dau wannan mataki.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai wasu 'yan majalisar wakilan Najeriyar suka soma sanya hannu kan tsige Shugaban Nigeriar bayan 'yan sanda sun hana kakakin majalisar wakilan shiga harabar majalisar.