Mutane 40 ne bam ya hallaka a Adamawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A cikin wannan makon ma, an kai hari a wata kasuwa a Maiduguri

Rahotanni daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nigeria na cewa mutane 40 ciki hadda soji biyar sun mutu sakamakon fashewar bam a gefen titi.

Bayanai sun ce lamarin ya auku ne a kusa da Mararrabar-Mubi, yankin da ake tashin hankali tsakanin dakarun kasar da 'yan Boko Haram.

Wani makanike Abubakar Adamu ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa motoci da dama sun kone sakamakon tashin bam din kusa da tashar motocin haya.

A halin yanzu dai daruruwan 'yan farauta da jami'an tsaro suna ci gaba da sintiri a wurare daban-daban na jihar Adamawa saboda yadda 'yan Boko Haram suke kai hare-hare.

Kungiyar Boko Haram ce keda iko a garuruwa da dama a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.