Ebola: An sami karuwar masu fama da cutar a Guinea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana cigaba da binciken maganin cutar yanzu haka

Ma'aikatan agaji a kudu maso gabashin Guinea ya ce ana samun karuwar masu fama da cutar ebola a yankin da cutar ta soma kuma har yanzu basu da isassun kayan aiki

Kungiyar Likitoci ta MSF da kuma kungiyar agajin Red Cross ta Faransa sun ce sun ga karuwar marasa lafiya a 'yan makonnin nan kuma duk da yake ana bude sabbin cibiyoyin magani amma sun cika makil cikin 'yan kwanaki.

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace cutar a Guinea na raguwa amma sai dai ta ruwaito cewa an sami karuwar wadanda suka kamu da cutar a Saliyo