An dage raba katunan zabe a Kaduna da Katsina

Hukumar zabe ta Najeriya (INEC) ta bayyana dage raba katunan zabe na dindindin da kuma fara yin rajistar wadanda ba su da katin zabe zuwa ranar 6 ga watan Disamba maimakon 28 ga watan da ake ciki.

A wani taron manema labarai a Kaduna, hukumar zaben ta bayyana cewa kalubalen aiki ne ya sanya wannan jinkiri a jihohin Kaduna da Katsina.

To sai dai tuni dai wasu 'yan siyasa suka fara nuna rashin amincewar su da wannan jinkiri.

Karo na uku ke nan ana dage raba katin zaben a jahar Kaduna abinda ya haifar da korafe korafe daga 'yan siyasa.