'Rashawa ta dabaibaye gwamnatin Jonathan'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ba shi ne karon farko ba da Obasanjo ke sukar gwamnatin Jonathan

Tsohon shugaban Nigeria, Cif Olusegun Obasanjo ya ce cin hanci da rashawa sun yi wa bangaren zartarwa da majalisar dokokin kasar.

Obasanjo ya fadi hakan ne a wajen bikin kaddamar da wani littafi a Abuja, babban birnin kasar ranar Laraba.

A cewarsa, "Idan kifi ya fara rubewa daga ka yake farawa."

Tsoshon shugaban ya yi nuni da cewa biyan 'yan majalisa kudadensu kai-tsaye ya taimaka wajen boye abubuwa marasa kyau da bangaren zartawa ke yi, hakan kuma ya sa majalisar ta gaza wajen sa ido a kan ayyukan ma'aikatu da hukumomin gwamnati, sai karbar na goro take yi daga gare su.

Game da batun rashin tsaro da ake fama da shi a kasar kuwa, Obasanjo ya gargadi gwamnati da cewa muddin aka ci gaba da amfani da karfi kadai wajen murkushe 'yan Boko Haram, to za a iya dakile ayyukan kungiyar na wani dan lokaci, amma ba za a iya kawar da matsalar baki daya ba.

Inda ya yi zargin cewa wasu a cikin gwamnati da kuma ita kanta Boko Haram suna amfana da rikicin.

Kazalika Cif Obasanjo ya ce ma'aunin tattalin arzikin da Najeriyar ke samu da ake ta ambatowa ba ya wani tasiri kan rayuwar mafi yawan talakawa da kuma masana'antu na kasar.