Za a samar da dokar mika bayanan sirri

A Burtaniya za a fitar da wata doka da za ta tilsatawa kanmfanonin sadarwa su dinga mika bayanan sirri kan masu amfani da na'urorin zamani.

A cewar hukumar tsaron cikin gida, wannan mataki zai kara karfafa matakan tsaron kasar.

Wannan doka za ta baiwa kamfanonin damar rike wasu bayanai da za su taimaka wajen gano masu amfani da na'urorin.

Sai dai masu kare hakkokin bil adama sun ce hakan zai sa ana bude bayanan sirri mutane.

Tun a jiya laraba ne aka aka mika kudirin wannan doka wacce za ta taimakawa 'yan sanda gano masu aikata laifuka ta hanyar yin amfani da na'urar kwamfuta da kuma wayoyi salula na hanu.

Bayanai na cewa kowace na'ura na da hanyar sadarwa na adreshin da za a iya ganowa ko mai amfani da ita ya kashe ko kuma ya kunna na'urar.

Yanzu haka dai babu wata kafa da zaa iya gano mai amfani da na'ura tare da nuna adreshin da aka baiwa mai amfani da ita.

Hakan kuma na nufin 'yan sanda ba za su iya gane mai amfani da na'urar ba.