Nijar: Briji Rafini ya tsira daga kuri'ar yanke kauna

Image caption Gwamnatin Nijar ta sha da kyar

A jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar wadda Firai minista Briji Rafini ke jagoranta ta kubuta daga yunkurin 'yan adawa na yanke mata kauna.

A karshen mahawarar da aka tafka, 'yan majalisar 75 ne suka yi watsi da bukatar 'yan adawan suna masu nuna goyon bayansu ga gwamnatin.

Sai dai 'yan adawan sun fice daga zauren majalisar kafin bayyana sakamakon, suna zargin masu rinjayen da tafka magudi.

An dai kwashe tsawon lokaci ana muhawara kafin daga bisana aka kada kuri'ar.