OPEC na yin taro kan farashin mai

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Farashin mai na ci gaba da faduwa a duniya

Ministocin kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur na duniya, OPEC na yin taro a Vienna, babban birnin Austria domin tattauna wa kan ko za su rage yawan man da suke hakowa domin zaburar da fashin mai a kasuwannin duniya.

Matsin tattalin arziki a nahiyar Turai da tafiyar hawainiyar da ake fuskanta a China da bunkasar man da kamfanin Shell na Amurka sun taimaka wajen faduwar farashin mai da kashi 30 cikin dari.

Ana sa rai kasashen Iran da Venezuela -- wadanda kudin shigarsu ke raguwa sakamakon faduwar farashin man -- za su bukaci a rage yawan man da kungiyar ke hakowa.

Kasar Saudi Arabia, wacce ke gaba wajen samar da mai a duniya, ba ta fayyace matsayinta ba.

Masu fashin-baki dai sun ce da wuya farashin mai ya wuce dala 100 a kan kowacce gangar mai daya idan ba wata hatsaniya aka samu a duniya ba.

Karin bayani