Madueke ta zama shugabar OPEC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mrs Diezani Alison-Madueke ta zama kallabi tsakanin rawwuna

Ministar man fetur ta Nigeria, Diezani Alison-Madueke ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur a duniya watau OPEC.

A ranar Alhamis aka zabi Alison-Madueke a taron kolin kungiyar da aka gudanar a Vienna babban birnin Austria.

Ta kasance mace ta farko da aka zaba domin rike wannan kujerar.

Madueke ta maye gurbin tsohon shugaban OPEC kuma dan kasar Libya, Abdourhman Atahar Al-Ahirish.

Ana saran za ta rike mukamin na tsawon shekara guda kafin a zabi wanda zai maye gurbinta.