An rufe shafukan masu satar fasaha

Wata kotu a Burtnaiya ta ba da umurnin rufe wasu shafukan masu satar fasaha da yawansu ya kai 53.

Wannan shine karo na farko da aka rufe shafuka da ake zargi da satar fasaha a fanninshirya fina-finai masu yawa kamar haka.

Bayanai kuma na cewa lamarin ya rutsa har da wasu manyan kamfanoni da suke samar da shafukan intanet su guda shida.

Sai dai kwararru a fagen sadarwa sun yi gargadin cewa har yanzu ba a tsira daga matsalar masu satar fasahar ba domin sukan nemi wata kafa su ci gaba da karya doka.

Kakakin kungiyar masu shirya fina-finai na Motion Pictures, wanda ya mika sunayen shafuka 32 cikin wadanda aka rufe ya ce an biciki shafukan inaten da dama ne lamarin da ya haifar da samun yawan wadanda aka rufe.

Daga cikin shafukan da aka dakatar da su daga bayyana a kafar ta intanet akwai Bitshop da IP Torrents da Isohunt da Sumotorrent da kuma Torrentdb.

Sauran sun hada da Torrentfunk da Torrentz da Warez BB da kuma Rapid Moviez.

"Wannan lamari ya mayar da hankali kan shafukan da ake amfani da gumin wasu ana neman kudi ba tare da samun su ya yi tasiri akan tattalin arzikin kasa ba." In ji daya daga cikin Shugabannin yankin nahiyar turai masu kula da lamarin, Chris Marcich.