'Biritaniya ta dauki matakai kan 'yan ci-rani'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cameron ya ce Biritaniya na son baki

Fira Ministan Biritaniya, David Cameron ya bayyana sabbin manufofinsa na rage yawan baki 'yan ci-rani daga kasashen Turai zuwa cikin Biritaniyar.

Mr Cameron ya ce kudaden tallafin da gwamnati ke bai wa jama'a, da ke kwadaitar da 'yan kasashen Turai zuwa Biritaniya, za a dakatar da su.

A cewarsa, sai baki daga kasashen Turai sun shafe shekaru hudu suna jira kafin an soma basu wasu kudaden tallafin gwamnati.

Mr Cameron ya ce sai baki daga kasashen Turai sun samu takardar soma aiki a Biritaniya kafin su shigo cikin kasar.

Sannan ya ce za a tisa keyar baki daga kasashen Turai da basu samu aikin yi ba a cikin watanni shida da shigowarsu cikin kasar.

Mr Cameron ya ce Biritaniya na son baki amma kuma dole ne a takaita tsarin domin a yi adalci.