Za a binciki mutuwar Thomas Sankara

Image caption Mr. Zida ya nemi Morocco ta tisa keyar Compaore gida idan kotun Burkina Faso ta bukaci hakan

Sabon Fira ministan Burkina Faso, Issac Zida ya ce gwamnati za ta sake binkicen musabbabin mutuwar tsohon shugaban kasar Thomas Sankara.

An dai kashe Sankara ne a shekarar 1987 a wani juyin mulkin da hambararren shugaba Blaise Compaore ya jagoranta, inda aka yi masa gunduwa-gunduwa aka binne shi a wani kabari da ba a yi wa shaida ba.

Bukatar bincika sanadin mutuwar tasa na daga cikin abubuwan da masu zanga-zanga a kasar suka gabatar.

Haka kuma Zida ya ce za a binciki kamfanoni da ma'aikatun gwamnati kuma duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa za a hukunta shi.