An kai harin bam a masallaci a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP

An kai hare-haren bam a masallacin gidan Sarkin Kano da ke arewacin Najeriya lokacin da ake sallar Juma'a.

Sama da mutane dari ne suka mutu a harin, kuma wasu dadama sun jikkata.

Bayanai sun ce bam din ya fashe ne lokacinda ake Sallar Juma'a.

Babban masallacin dai shi ne inda mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya ke Sallah inda a wani karon ma shi ne ke yin limanci.