Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bam ya tashi a masallaci a Kano

Hakkin mallakar hoto Babayo Tahir

An kai hare-haren bam a masallacin gidan Sarkin Kano dake arewacin Najeriya lokacinda ake sallar Juma'a.

Har yanzu dai ba'a kaiga tantance adadin wadanda suka rasu ba amma dai rohotanni na cewa akalla mutane 90 ne suka hallaka.

Bayanai sun ce bam din ya fashe ne gabanin a kai ga fara Sallah juma'a.

Babban masallacin dai shi ne inda mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya ke Sallah inda a wani karonma shi ne ke yin limanci.

Harin na zuwa makonni bayan da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci mutane su kare kansu daga hare-hare Boko Haram.