Harin Kano: Sarki ya ce kada a karaya

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga jama'ar Jihar da kada su bari harin da aka kai ranar juma'a ya hana su gudanar da harkokinsu na yau-da-kullum.

Sarkin na jawabi ne a lokacin da tsohon shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari ya kai masa ziyarar jaje.

Sarkin yace:" bayan addu'o'i da akeyi, a daure, a cigaba da harkoki na yau da kullum da mu'amaloli da aka saba amma tare da yin hattara".

Sarkin dai har sai da ya zubar da hawaye a lokacin da yake jawabi.

A jiya ne sarkin ya katse aikin umra da ya keyi a Saudiyya, kuma bayan ya dawo shine yayi limanci a masallacin da aka kai harin a lokacin sallar Magaruba.

Sama da mutane dari ne suka a mutu a harin na ranar Juma'a.

Wasu dadama kuma da suka samu raunuka a harin na kwance a asibiti yanzu haka.

Shaidu sun ce maharan sun tada bama-bamai ne a masallacin bayan an tada sallah.

Sun bada labarin harbe-harbe da wasu 'yan bindiga su ka yi bayan bama-bama sun tashi.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin, ya kuma bayanashi da cewa wani aikin rashin imani ne.

Ya kuma sha alwashin gano wadanda suka kai harin

Karin bayani